Atiku ya zargi Tinubu da ɓoye bayanan sabon bashin waje na dala biliyan 21.6


Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ɓoye cikakkun bayanai kan shirin neman sabon bashin waje da ya kai dala biliyan 20.52 da kuma Yuro biliyan 1.045, yana mai gargaɗin cewa akwai yiwuwar karkatar da kuɗaɗen domin biyan muradun siyasarsa.    



Atiku ya bayyana wannan matsaya ne bayan Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin karɓar bashin a ƙarƙashin shirin samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan gwamnati.


Hamada Reporters ta ruwaito cewa Atiku ya nuna damuwarsa kan rashin bayyana cikakkun bayanai game da bashin, yana mai cewa ya kamata a fayyace yadda za a yi amfani da kuɗaɗen da kuma ayyukan da za a gudanar da su da su.


Me za ku ce?

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org