Ƴansanda sun kama matashi ɗan agaji da ake zargi da kiran a kashe Kiristoci a wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta.
Rundunar ƴansandan Jihar Zamfara ta kama wani matashi mai suna Umar Ibrahim Gandi Maradun, bisa zargin yin kiraye-kirayen kashe Kiristoci a wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta.
A cikin sanarwar da Kwamishinan ’yansandan jihar, A.M. Bello, ya fitar ranar Talata, 27 ga Oktoba, 2026, rundunar ta ce bidiyon ya nuna matashin sanye da kayan ƙungiyar JIBWIS, yana rera waƙar neman a ba su bindigogi domin su je su kashe Kiristoci.
Binciken farko ya nuna cewa an ɗauki bidiyon ne ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, lokacin da ake zargin matashin yana kan hanyarsa ta zuwa Masallacin Aliyu Ibn Abi Thalib domin gudanar da ayyukan tsaro yayin sallar Juma’a da wa’azi.
Ƙungiyar JIBWIS ta nesanta kanta da abin da ke cikin bidiyon, sannan ta kama wanda ake zargin tare da miƙa shi ga ’yansanda domin gudanar da bincike.
Rundunar ta tabbatar da cewa ta fara bincike kan lamarin, tare da jaddada aniyarta ta kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba tare da nuna bambanci na addini ba.