Gwamna Radda Ya Halarci Bikin ’Ya’yan Minista Noma Abubakar Kyari

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya halarci ɗaurin auren Muazu Abubakar Kyari da Ibrahim Abubakar Kyari, ’ya’yan Mai Girma Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari.


An gudanar da bikin ne bayan sallar Juma’a a Masallacin Alfurqan a Jihar Kano, inda Gwamna Radda da sauran manyan baƙi suka halarci bikin domin taya ma’auratan murna.



Bikin ya samu halartar Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum; Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, Kauran Gwandu; da Gwamnan Jihar Neja, Hon. Mohammed Umaru Bago, tare da sauran manyan jami’an gwamnati da ’yan siyasa na yanzu da na baya.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org