Yadda wasu Iyaye suka Rasa 'ya'yan su biyu ta hanyar Kisan Gilla a Katsina
Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Wasu iyaye a garin ’Yar Liya’u da ke Ƙaramar Hukumar Kurfi a Jihar Katsina sun shiga cikin jimami bayan an kashe ’ya’yansu biyu masu ƙananan shekaru, waɗanda suka fita kiwon awaki amma ba su dawo gida ba.
Yaran, Nura Abdulrashid mai shekaru takwas da Safiyya mai shekaru 10, an same su ne a ranar Lahadi, 6 ga Satumba, 2026, bayan wani bincike da al’ummar garin suka gudanar.
Mahaifin Nura, Abdulrashid Suleman, ya shaida wa Katsina Times cewa ya bar ɗansa a gida da safe lokacin da yake shirin zuwa gona.
Ya ce Nura ya bi shi na ɗan lokaci yana yi masa bankwana, kafin daga bisani ya koma gida.
Abdulrashid ya ce lokacin da ya dawo daga aiki da yamma, ya tambayi inda ɗansa yake, inda aka sanar da shi cewa Nura ya fita kiwo tare da Safiyya.
“Awakin sun dawo amma yaran ba su dawo ba. Sai na je ofishin ’yan sanda da ke Kurfi na kai rahoton cewa yaran sun fita kiwo tun safe amma ba a gan su ba,” in ji shi.
Ya ce daga bisani mazauna garin suka shiga neman yaran, inda aka fara samun gawar Nura a wani wuri da ke cikin daji.
A cewarsa, an kuma gano gawar Safiyya a wani wuri daban.
Mahaifin ya bayyana cewa yadda aka kashe yaran ya jefa iyalan cikin firgici, yana mai roƙon jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike tare da gano waɗanda ke da hannu a lamarin.
Aminu Ibrahim, wanda ya kasance uba ga Safiyya bayan rasuwar mahaifinta, ya ce al’ummar garin ba su san wanda za su zarga ba, amma ya buƙaci hukumomi su binciki lamarin domin tabbatar da adalci.
Ita ma mahaifiyar Nura, Ladidi, ta bayyana matuƙar baƙin cikinta tare da yin kira ga gwamnati da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam su taimaka wajen ganin an gano waɗanda suka aikata kisan.
Dattawa da limaman garin ’Yar Liya’u sun kuma buƙaci hukumomin tsaro su zurfafa bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu.
Rahotanni sun ce an gano awakin biyu da yaran ke kiwo a hannun wani direba, wanda ya shaida cewa wani fasinja ne ya tsayar da shi ya ba shi awakin domin ya kai su kasuwa.
Direban ya ce fasinjan ya gudu bayan motarsa ta samu matsala, inda ya bar shi da awakin, yana mai cewa bai san mutumin ba kuma bai taɓa ganinsa a baya ba.
Jami’an tsaro sun ziyarci garin ’Yar Liya’u tare da tattara bayanai daga mazauna domin gudanar da bincike kan kisan.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana wanda ake zargi da kisan ko cikakken dalilin da ya kai ga kashe yaran ba.

