Iyalan El-Rufai Sun Ba Christopher Musa Wa’adin Kwanaki Bakwai
Iyalan tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, sun bai wa Ministan Tsaro, Christopher Musa, wa’adin kwanaki bakwai ya janye wani zargi da suka ce ya yi wa tsohon gwamnan, ko kuma su garzaya kotu.
A cikin wata sanarwar manema labarai da Hon. Mohammed Bello El-Rufai ya fitar a madadin iyalan ranar Litinin a Abuja, iyalan sun ce sun damu matuƙa da kalaman da ministan ya yi game da tsohon gwamnan.
Iyalan sun ce kalaman sun shafi zargin cewa El-Rufai ya shirya hallaka wasu mutane a Kudancin Kaduna. Sun bukaci ministan ya janye wannan zargi tare da gyara kalamansa cikin wa’adin da suka gindaya.
A cewar sanarwar, kalaman sun fito ne a ranar 3 ga Satumba, 2026, yayin wani shirin kai-tsaye na “Politics Today” na gidan talabijin na Channels. Iyalan sun bayyana cewa idan ba a janye kalaman cikin kwanaki bakwai ba, za su ɗauki matakin shari’a kan lamarin.
#Danmasani Radio#ElRufai #NasirElRufai #ChristopherMusa #Kaduna #KudancinKaduna #Nigeria #Tsaro #SiyasarNigeria #PoliticsToday #HausaNews #NigeriaNews
