Gwamnatin Tarayya ta bayyana yadda za a inganta amfani da Tsarin Haɗa Bayanai da Biyan Albashin Ma’aikata.

 Shugaban Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (FCSC), Farfesa Tunji Olaopa, ya bayyana yadda za a inganta amfani da Tsarin Haɗa Bayanai da Biyan Albashin Ma’aikata (IPPIS) domin amfani ga ma'aikatan gwamnati.



Olaopa ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin bikin ƙaddamar da fara aiki da sassan kula da harkokin ma’aikata na IPPIS, wanda Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Misis Didi Esther Walson-Jack, ta jagoranta.


Olaopa ya ce cikakken tsarin sassan kula da harkokin ma’aikata na IPPIS ya ta’allaka ne kan ƙirƙire-ƙirƙire wajen gudanar da sauye-sauye, domin a magance gibin da ake da shi a yanzu tare da amfani da damar da ke akwai wajen tabbatar da cewa an aiwatar da tsarin gaba ɗaya a dukkan sassan gwamnati.


Ya ƙara da cewa hakan ya kamata ya haɗa da tabbatar da ingancin bayanai, ƙara ƙarfin tsarin IPPIS, da kuma faɗaɗa amfanin da shi, domin kawo sauyi da inganta tsarin gudanar da harkokin gwamnati baki ɗaya.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org