Yan Sanda Sun Fara Farautar wadanda suka Sace Ɗaliban Jami’ar Tarayya Ta Lafia

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa ta fara farautar masu yan ta’addan dasukayi garkuwa da ɗalibai uku na Jami’ar Tarayya da ke Lafia.




An sace ɗaliban ne a Dakin kwanan daliabai da ke Sure Leaders Lodge a yankin Bukan Kwato, kusa da harabar jami’ar, da misalin ƙarfe 8:45 na daren Asabar.


Kakakin rundunar, SP Ramhan Nansel, ya ce ana gudanar da bincike da kuma aikin ceto domin kubutar da ɗaliban cikin ƙoshin lafiya tare da cafke masu laifin.


Ya ƙara da cewa har yanzu ba a kama kowa ba, amma jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ganin an sako ɗaliban cikin gaggawa.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org