Mutumin da yafi kowa tsayi a Ghana ya rasu.
Mutumin da ya fi kowa tsayi a ƙasar Ghana, Sulemana Abdul Samed, wanda aka fi sani da Awuche, ya rasu yana da shekara 33 a duniya.
Rasuwarsa ta haifar da alhini da jimami matuƙa, musamman a arewacin Ghana, inda tsayinsa na ban mamaki ya sa ya zama sanannen mutum a yankin.
Manema labarai sun rawaito a yammacin ranar Talata, Awuche ya rasu ne a ranar Litinin a Asibitin Koyarwa na Tamale, bayan an kwantar da shi saboda ƙafafunsa da suka kamu da cuta.
Yayi jinya a birnin Tamale da ke arewacin ƙasar, mai nisan kusan kilomita 160 daga ƙauyensu na Gambaga.
