Da Lawan Ahmad Ya Cigaba Da Fim Da YouTube, Da Yafi Masa Fiye Da Shiga Siyasa" - Inji Adam A. Zango
Jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya bayyana cewa Lawan Ahmad ya samu daraja da kima sosai sakamakon rawar da ya taka a shahararren fim ɗin Izzar So. A cewarsa, da Lawan ya ci gaba da mayar da hankali kan harkar fim da kuma bunƙasa tasharsa ta YouTube, da hakan ya fi masa amfani fiye da shiga siyasa kai tsaye.
Zango ya ce shiga siyasa ya sa Lawan Ahmad ya rasa wani ɓangare na kimar da ya gina a idon masoyansa, yana mai cewa idan shi ne a matsayinsa, da ya ci gaba da fitar da sabbin ayyukan fim a YouTube domin samun ci gaba mai ɗorewa, maimakon dogaro da 'yan siyasa.
"Da ni ne shi, da na riƙe YouTube ɗina ina fitar da sabbin ayyuka da zasu taimaka min. Bin 'yan siyasa ba zai baka abin da zaka iya samu ta hanyar fim ba," in ji Adam A. Zango.

