Babu kyakkyawar budurwa a garin Musawa da ta kai Hajiya Indo Musawa.
KO BA MUTUWA, AKWAI TSUFA
![]() |
A wancan lokaci an ce babu kyakkyawar budurwa a garin Musawa da ta kai Hajiya Indo Musawa. Kyawunta yayi fice har yasa fitaccen mawaƙin hausa marigayi Dr. Mamman Shata, yayi mata waƙa inda ya yabe ta da kuma kyawun halayenta.
A cikin waƙar ya ce: "Wata 'yar yarinya, mai kyau diri da kyau tsari, mai kyau zama da kyau tafiya, ga alkawari kamar tawada, ga daɗin riƙo kamar chasbi, Indon Musawa."
Yau kuwa shekaru sun shuɗe lokaci yayi aikinsa, kuma tsufa ya maye gurbin ƙuruciya. Wannan wani babban darasi ne ga kowa.
Hakika, duk wanda aka ba tsawon rai zai ga yadda ƙuruciya ke shuɗewa, kyawu ya ragu, ƙarfi ya dusashe, sai ayyukan alheri da kyawawan ɗabi'u su ragewa mutum abin tunawa.
Lallai, ko ba mutuwa, akwai tsufa. Allah ya sa ƙarshenmu ya zama mai kyau Amin.
Hoto: Hausa Channel

