Ministan Yaɗa Labarai Ya Yaba Da Sabon Ɗakin Watsa Labarai na Zamani na NTA da Gyaran Cibiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana gamsuwar sa kan sabon ɗakin watsa shirye-shiryen talbijin na zamani da aka kammala a hedikwatar Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA), tare da cigaban da aka samu a aikin gyaran Cibiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa (National Press Centre).
Idris, wanda ya bayyana cewa waɗannan ayyuka hujja ne ƙarara da ke nuna ƙudirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na zamanantar da cibiyoyin yaɗa bayanai na gwamnati, ya bayyana haka ne a ranar Litinin bayan ya duba waɗannan cibiyoyi da ke Abuja.
A cewar sa, waɗannan zuba jari wani ɓangare ne na ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na sake fasalta kafafen yaɗa labarai na gwamnati domin su samar wa da 'yan Nijeriya ingantaccen aikin watsa shirye-shirye da yaɗa bayanai.
Ya ce: "Abin da muka gani a yau cika alƙawarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne na zamanantar da cibiyoyin watsa shirye-shiryen gwamnati a Nijeriya. Wannan yana ɗaya daga cikin mafi kyawun ɗakunan watsa shirye-shirye a Nijeriya, kuma yana cikin mafi inganci a nahiyar Afrika."
Ministan ya ce sabon situdiyon yana cikin mafi ingancin cibiyoyin watsa shirye-shirye a Afrika, kuma wani ɓangare ne na babban shirin zuba jari da ake aiwatarwa a NTA, Gidan Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), Muryar Nijeriya (VON) da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN).
Ya yaba wa shugabanni da ma'aikatan NTA bisa goyon bayan da suke bai wa shirin sauye-sauyen, yana mai cewa gyaran ba ya tsaya kan gine-gine kawai, har ma ya shafi inganta shirye-shirye, ƙwarewar aiki, ƙirƙire-ƙirƙire da bunƙasa ƙwarewar ma'aikata.
Ya ce aikin sayo sababbin kayan aikin watsa shirye-shirye na zamani ga tashoshin NTA a faɗin ƙasar nan, tare da irin wannan zuba jari a sauran kafafen yaɗa labarai na gwamnati, zai inganta matuƙa aikin watsa shirye-shiryen hidimar jama'a a Nijeriya.
Idris ya bayyana cewa sake ƙaddamar da shirin sauya fasahar watsa shirye-shiryen talbijin daga analog zuwa dijital (Digital Switch Over – DSO) wata babbar nasara ce wadda ke ƙara ƙarfafa shirin zamanantar da harkar watsa shirye-shirye a Nijeriya.
Ya ce: "Shirin 'Digital Switch Over' da kuma zuba jari a sababbin kayan aikin watsa shirye-shirye sun buɗe sabon babi ga fannin yaɗa bayanai a Nijeriya. Da zarar an kammala wannan shirin gyare-gyare, 'yan Nijeriya za su shaida cikakken sauyi a tsarin watsa shirye-shiryen gwamnati."
Ministan ya kuma bayyana cewa Shugaba Tinubu ya himmatu wajen inganta walwalar ma'aikatan fannin yaɗa labarai, yana mai jaddada cewa gwamnatin na fahimtar muhimmancin zuba jari ba kawai a gine-gine da kayan aiki ba, har ma a kan ma'aikata.
Bayan kammala duba cibiyoyin NTA, Ministan ya ziyarci Cibiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa da ke Radio House, inda ya nuna gamsuwa da yadda aikin gyaran yake tafiya.
Ya ce sabuwar Cibiyar 'Yan Jaridar za ta zama cibiyar aikin kafafen yaɗa labarai ta zamani mai ɗauke da kayan aiki na duniya da kuma intanet mai saurin gaske domin taimaka wa 'yan jarida masu bibiyar harkokin gwamnati da manyan abubuwan da ke faruwa a ƙasa.
Ya ce: "Dole ne Cibiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa ta cika manufar ta ta kasancewa babbar cibiyar aikin kafafen yaɗa labarai a Nijeriya. Ana sake fasalta ta ne domin samar wa 'yan jarida da yanayi mai kyau da kuma kayayyakin zamani da za su taimaka masu wajen gudanar da aikin su yadda ya kamata."
Ministan ya buƙaci 'yan kwangilar da ke aikin da su kammala shi a cikin wa'adin da aka tsara, yana mai cewa zai sake dawowa domin yin dubawar ƙarshe kafin a ƙaddamar da cibiyar.
Ya sake jaddada cewa gyare-gyaren da ake yi a kafafen yaɗa labarai na gwamnati suna nuna ƙudirin Shugaba Tinubu na ƙarfafa sadarwa da jama'a, inganta yaɗa sahihan bayanai da kuma ɗaga darajar fannin yaɗa labarai na Nijeriya zuwa matakin ƙasa da ƙasa.

