Yadda Aka Hallaka Dalibin Jami'ar Jos Kan Zargin Satar Wayar Iphone 12

 Wani matashi mai suna Ibrahim Mbaya, ɗan shekara 25, wanda ya kammala karatu a Jami'ar Jos (UNIJOS) kuma fitaccen mai yin tallan kaya (model), ya rasu bayan da ake zargin wasu matasa sun yi masa dukan tsiya kan zargin satar wayar iPhone a birnin Jos, jihar Filato.


Rundunar 'Yan Sandan Jihar Filato ta tabbatar da kama mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin. Kakakin rundunar, SP Alfred Alabo, ya ce an kai Mbaya Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jos (JUTH), inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.


A cewar 'yan sanda, binciken farko ya nuna cewa an yi wa marigayin dukan ne bayan an zarge shi da satar wayar salula, maimakon a miƙa shi ga jami'an tsaro domin gudanar da bincike bisa doka.


An miƙa waɗanda aka kama zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) domin ci gaba da bincike, yayin da ake ci gaba da neman sauran waɗanda ake zargin sun tsere bayan aukuwar lamarin.


Rundunar 'yan sandan ta yi Allah wadai da abin da ta kira ɗaukar doka a hannu (jungle justice), tare da jan hankalin jama'a da su riƙa kai rahoton duk wanda ake zargi da aikata laifi ga jami'an tsaro maimakon hukunta shi da kansu.


Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike kan lamarin. 


Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org