Duk abin da ya faru ga El-Rufai to laifin Tinubu ne - ADC
Jam'iyyar ADC ta zargi gwamnatin tarayya da tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, saboda dalilai na siyasa, tana mai cewa ana son hana shi taka rawa a zaɓen 2027.
Mai magana da yawun jam'iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya ce idan wani abu ya samu El-Rufai yayin da yake tsare, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne za a ɗora wa alhakin hakan.
Abdullahi ya bayyana cewa ci gaba da tsare El-Rufai ba tare da beli ba na nuna cewa manufar gwamnati ita ce raunana 'yan adawa, yana mai cewa idan zarge-zargen da ake masa na laifi ne, kotu ce ya kamata ta yanke hukunci.
Ya kuma yi iƙirarin cewa lafiyar El-Rufai ta tabarbare a tsare, tare da roƙon gwamnatin tarayya ta sake shi beli domin ya ci gaba da kare kansa a kotu.
Sai dai El-Rufai na fuskantar tuhume-tuhume daga Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da kuma Hukumar ICPC kan zarge-zarge daban-daban, yayin da kotu ta ƙi amincewa da buƙatarsa ta beli a farkon wannan wata.
