An kama sojan da ake nema ruwa a jallo yana ƙoƙarin tserewa zuwa Kamaru

 Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da kama wani soja mai suna Private Mohammed Yusuf, wanda aka ayyana ana nema bisa zargin sayar da kayan aikin soja ga 'yan ta'adda da sauran masu aikata laifuka.


A wata sanarwa da rundunar Operation HADIN KAI ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an kama sojan ne a tashar mota ta Jidari da ke Maiduguri yayin da ake zargin yana ƙoƙarin tsallakawa zuwa Jamhuriyar Kamaru.


Jami'in yaɗa labarai na rundunar a Arewa maso Gabas, Kyaftin Muhammed Goni, ya ce binciken farko ya nuna cewa Yusuf ya gudu daga sansaninsa tun ranar 7 ga Yulin 2026, sannan ya buya a unguwar Gomari Costain da ke ƙaramar hukumar Jere.


Ya ce sojoji sun kama shi ne bayan samun sahihan bayanan sirri, kuma ana ci gaba da bincike domin gano cikakken rawar da ya taka da kuma ko akwai wasu da suka haɗa kai da shi.


Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da hukunta duk wani jami'inta da ke da hannu a ayyukan da ke barazana ga tsaro, tare da kira ga jama'a su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org