Taron COP 31 a Antalya, Ƙasar Turkiyya

A yau, tawagar Hukumar Sauyin Yanayi ta Jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Sauyin Yanayi, Farfesa Al’amin Muhammed, da Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Sauyin Yanayi, Alhaji Suleiman S Ribadu, ta halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi, da ke gudana a birnin Antalya, na Kasar Turkiyya.



Cikin mahalarta taron akwai Babban Mai Taimakawa Gwamna kan Kafafen Sadarwa, Engr. MS Ingawa. 


Taron, ya haɗa shugabannin ƙasashe, masana kimiyya, shugabannin harkokin kasuwanci, ƙungiyoyin farar hula, da ƙungiyoyin matasa da mata daga sassa daban-daban na duniya, domin ƙarfafa matakan yaƙi da sauyin yanayi da bunƙasa haɗin gwiwar ƙasashe.



Kamar yadda aka saba a tarurrukan baya, taron na bana ya zama muhimmiyar kafa ta duniya wajen musayar dabaru, tsara manufofi da bunƙasa sabbin fasahohi domin cimma muradun Yarjejeniyar Paris (Paris Agreement), rage ɗumamar yanayi da kuma ƙarfafa juriyar al’umma da muhalli ga illolin sauyin yanayi.


Ƙarƙashin taken “Inda Tattaunawa ke Zama Aiki” (Where Dialogue Becomes Action), an bayyana COP 31 a matsayin taron aiwatar da alkawura (Implementation COP), wanda zai mayar da hankali kan mayar da alkawuran da aka ɗauka a baya zuwa ayyuka da za su haifar da sakamako a zahiri.


An tsara taron ne bisa manyan jigogi guda 10 wanda ya ƙunshi muhimman fannoni kamar rage yawan zubar da shara, sauya fasalin samar da makamashi zuwa makamashi ta hanya mai tsafta, bunƙasa masana’antu masu kare muhalli, samar da wadataccen abinci, matasa da ilimi, da sauran fannoni masu muhimmanci.


A yau, tawagarmu ta halarci muhimman tarurruka da dama, waɗanda suka haɗa da tattaunawar ƙwararru, gabatar da takardu da nazarce-nazarce kan sauyin yanayi. Waɗannan tarurruka suna samar da damammaki masu muhimmanci wajen tallata manufofi da ayyukan Jihar Katsina, kalkashin jagorancin gwamna Malam Dikko Umaru Radda, a fannin sauyin yanayi, jawo hankalin masu zuba jari, da samar da hanyoyin haɗin gwiwa da manyan masu ruwa da tsaki na duniya domin inganta yaƙi da sauyin yanayi da kuma tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.


A wajen tattaunawar mun gabatarwa da masu ruwa da tsaki irin gagarumin cigaba da jihar Katsina ta samu a fannin sauyin yanayi ciki harda kasancewarta jiha ta farko a Nigeria a bangaren dabbaka harkokin sauyin yanayi wanda ta zaburo daga mataki na 30 a shekara biyu da suka wuce. 


Tattaunawar zata cigaba na tsawon lokaci..


MS Ingawa

SSA, Media & Strategy

Katsina State Government


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org