Gwamnatin Tarayya ta amince za ta riƙa biyan ma’aikata alawus ɗin sufuri na ₦70,000 duk wata na tsawon watanni shida,
Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan Kudaden tallafin Sufuri da ya kai Naira Dubu 70 duk karshen Wata ga ma’aikatan Gwamnati na tsawon watanni shida, a wani mataki na rage wa Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya raɗaɗin tsadar rayuwa a Fadin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa an cimma matsayar ne bayan ganawar da wakilan Gwamnatin Tarayya da shugabannin Ƙungiyoyin Kwadago ta Najeriya (NLC) suka yi a Abuja, a Talatar nan.
A yarjejeniyar da aka cimma, Gwamnatin Tarayya zata fara biyan tallafin ne daga watan Nuwamba Mai zuwa, inda ma’aikata za su ci gajiyar tallafin na tsawon watanni shida kacal.
Bayan haka, Gwamnatin ta amince da biyan bashin wasu alawus-alawus na musamman da Ma'aikatan ke bin ta, wanda lissafin zai faro tun daga Ranar 1 ga Watan Mayun da ta gabata. Za a biya bashin ne kashi-kashi har sau uku, daga Watan na Nuwamba.
Sai dai, bangarorin biyu ba su cimma matsaya kan Ranar da za a fara aiwatar da sabon ƙarin mafi ƙarancin albashi na ƙasa Baki Daya ba.
Duk da haka, sun aminta da kafa kwamitin tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi, wanda zai fara aiki nan take domin ci gaba da tattaunawa kan batun da Ƙungiyoyin Kwadago suke Bukata a aiwatar Kafin Babban Zaben Watan Janairun 2027.
Taron ya samu halartar jami’an Gwamnatin Tarayya da wakilan ƙungiyoyin kwadago, ciki har da Ministan Kwadago, Dakta Muhammad Maigari Dingyadi, da Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC, Mista Joe Ajaero.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ma’aikata ke fuskantar ƙalubalen tsadar Man Fetur, sufuri, kayan abinci da sauran kayayyakin amfanin Yau da kullum, tun bayan cire tallafin Man Fetur da Gwamnati Mai ca ta yi, lamarin da ya ƙara jefa iyalai da dama cikin matsin tattalin arziki.
.jpg)