Ana fargabar wani ɗan sanda ya harbe abokiyar aikinsa sannan ya harbe kansa a sansanin ASCO da ke Ajaokuta

 Ana fargabar wani ɗan sanda ya harbe abokiyar aikinsa sannan ya harbe kansa a sansanin ASCO da ke Ajaokuta, Jihar Kogi, inda jami'an biyu suka rasu sakamakon lamarin.



Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan, Saliu Oyiza Afusat, ta fitar kan mutuwar jami'an.


Ta ce, Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a, 23 ga Oktoba, 2026, inda binciken farko ya nuna cewa Kofur Amos Yusuf, wanda ke aikin dare, ya harbi wata ’yar sanda mai suna Kofur Grace Onimisi, sannan ya harbe kansa.


Sanarwar ta ce, an kai jami'an 2 asibitoci daban-daban, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu. 


Rundunar ta ce, an ajiye gawawwakinsu a ɗakin ajiyar gawa na Asibitin ASCO, yayin da jami'an ’yan sanda suka ƙwato bindigar AK-47 da harsashi huɗu da aka harba a wurin.


Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kogi, Naziru Bello Kankarofi, ya miƙa ta'aziyya ga iyalan jami'an. 


Me za ku ce?



Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org