Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Ta Yi Gargadin kasancewar Annobar Ebola Ta Zama Mai Sarƙaƙiya a Afirka Bayan Najeriya Ta Tabbatar da bullarta.



Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin cewa, Nahiyar Afirka na fuskantar annobar Ebola mai sarkakiya, bayan da cutar ta bazu daga Gabashin Afirka zuwa Najeriya, wadda ta tabbatar da samunta a karin farko a yankin Yammacin Nahiyar.

Daraktan hukumar  ta WHO mai kula da yankin Afirka Mohamed Janabi  ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar ta yanar gizo.

Janabi ya ce, “Yanzu muna fuskantar yanayin annoba mai sarkakiya. Najeriya ta tabbatar da samun mutum guda da ya kamu da cutar Ebola daga wata ƙasa.”

A ranar Talatar da ta gabana ne, Najeriya ta sanar da gano bullar cutar a karon farko, mai nau’in 'Bundibugyo' wandda ke da alaƙa da babbar annobar da ta ɓarke a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.Wata  ma'aikaciyar diflomasiyya ce wadda ta taɓa yin balaguro zuwa Uganda ta kamu da cutar.

Najeriya wadda ita ce ƙasa mafi yawan al’umma a Afirka, ta zama ƙasa ta huɗu a Nahiyar da annobar ta shafa. A wannan makon ne cutar ta bazu zuwa ƙasashen Gabashi da Yammacin Afirka, inda Kenya ta sanar da samun mutum tara da suka kamu da cutar tun ranar 6 ga wannan wata na Oktoba.

Samun wannan bullar cuta, ya sake tayar da tunanin mummunar annobar Ebola da ta ɓarke a shekarar 2014, wadda ta shafi ƙasashe da dama a yankin Yammacin Afirka, tare da kashe mutane fiye da 11,000 tsakanin ƙarshen shekarar 2013 da 2016.


Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org