Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya danganta rashin wutar lantarki a yankunan karkara da yin barci da wuri,

 Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya danganta rashin wutar lantarki a yankunan karkara da yin barci da wuri, rashin nishaɗin dare da kuma ƙarin yawan haihuwa a tsakanin al’umma.


Fayose ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Juma’a, jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban hukumar samar da wutar lantarki a yankin karkara wato Rural Electrification Agency (REA).




Ya ce rashin wutar lantarki na sa mazauna karkara komawa gida da wuri, domin babu wasu abubuwan nishaɗi da za su shagaltar da su da dare.


A cewarsa, samar da wutar lantarki a yankunan karkara zai bunƙasa harkokin dare da nishaɗi, tare da samar wa mutane wasu hanyoyin shakatawa.


Fayose ya yi wannan jawabi ne yayin da ya fara jagorantar hukumar da ke da alhakin faɗaɗa samar da wutar lantarki ga al’ummomin da ba su da cikakkiyar damar samun wuta a Najeriya.


Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya rantsar da Fayose da sauran mambobin sabuwar hukumar. An kuma naɗa Abba Aliyu a matsayin Darakta Janar na hukumar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org