Mu Malaman FUDMA Ba Mu Aike Ka Ka Zama PRO ɗinmu Ba,— Martanin Malami Ga Shugaban Hukumar Hisbar Katsina Kan Jawabin Goyon Bayan Tinubu.

 Mu Malaman FUDMA Ba Mu Aike Ka Ka Zama PRO ɗinmu Ba,— Martanin Malami Ga Shugaban Hukumar Hisbar Katsina Kan Jawabin Goyon Bayan Tinubu.



Wani malami a Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA), Malam Ibrahim Bature, ya yi wa Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Sheikh Abu Ammar, gargadi kan yadda yake tsoma baki cikin harkokin siyasa, yana mai cewa bai kamata ya rika magana da sunan malaman jami’ar ba.


Bature ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya yi kira ga Abu Ammar da ya daina rantsuwa yayin magana kan siyasa, tare da jaddada muhimmancin tsoron Allah wajen furta kalamai kan al’amuran jama’a.


A cewar Bature, “Aminina, Sheikh Abu Ammar, a daina rantsuwa a cikin siyasa, babu kyau. Sannan ka ji tsoron Allah.” In ji shi


Malamin ya kuma yi watsi da duk wani ra’ayi da zai nuna cewa Abu Ammar na magana a madadin malaman FUDMA, yana mai cewa ba su ba shi izinin zama kakakin ra’ayinsu ba.


“Mu Malaman FUDMA ba inda muka aike ka ka zama PRO namu, ka rika faɗin abin da ba ra’ayinmu ba ne,” in ji shi, yana mai bayyana cewa ra’ayinsa ne na kansa, don haka kar a ɗauki maganganunsa a matsayin matsayar malaman FUDMA baki ɗaya ba.


Bature ya kara da cewar wanda yake tsoron Allah ya kamata ya fahimci irin halin da talakawa ke ciki, yana mai cewa duk da fatan samun sauyi a ƙasa, jama’a na ci gaba da fuskantar matsaloli.


“Duk mai tsoron Allah ya san yanayin da talakawa ke ciki. Ni da kai, mun iya cewa Allah Ya kawo mana canji a rayuwarmu a cikin wannan ƙarni na Tinubu, amma al’ummah na cikin masifa.” In ji shi

Jaridar Taskar Labarai 

Har wayau, a cikin sakon nasa, Malam Bature ya kuma yi nuni da wani hari da ya ce ’yanbindiga sun kai a wani ƙauye da ke bayan Take-Off Site na FUDMA, a yankin Maitsani, yana mai cewar an kashe wasu mutane a harin, kuma wurin da lamarin ya faru yana da nisan kusan kilomita biyu daga jami’ar, "amma ka fito kana irin wannan. Mallam, ka ji tsoron Allah,” in ji Bature.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org