Kotun Ƙasar Syria ta yanke wa Tsohon Shugaban Ƙasa Bashar Al-Assad, hukuncin Kisa a hukumance.

 Wata kotu a Syria ta yanke wa tsohon Shugaban ƙasar, Bashar al-Assad, hukuncin kisa a ranar Talata, bayan ta same shi da laifukan da suka haɗa da kisan gilla, azabtarwa, kama mutane ba bisa ƙa’ida ba da kuma laifukan cin zarafin bil’adama.


An yanke hukuncin ne a rashin halartar Assad a kotu, yayin da yake gudun hijira a Rasha. Wannan shi ne hukuncin farko da aka yanke wa Assad tun bayan hambarar da gwamnatinsa a watan Disambar 2024. 


Bayan faduwar gwamnatinsa, Assad ya tsere daga Damascus zuwa Moscow tare da iyalansa, inda Rasha ta ba shi mafaka.


Kotu ta kuma yanke irin wannan hukunci ga Maher al-Assad, ƙanin Bashar, da kuma wani tsohon jami’in tsaro, Atef Najib, wanda ya kasance cikin jami’an da ake zargi da murkushe zanga-zangar da ta fara a birnin Daraa a shekarar 2011.


Hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da sabuwar gwamnatin Syria ke ƙoƙarin gurfanar da wasu daga cikin manyan jami’an tsohuwar gwamnatin Assad bisa zargin aikata laifukan yaƙi da take haƙƙin bil’adama.


Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org