Dalibar FULAFIA Ta Rasa Rai A Hanyar Keffi Zuwa Lafia
Dalibar aji 400 ta Jami’ar Tarayya da ke Lafia (FULAFIA), Habiba Ummi Lele, ta rasu bayan an kai wa motar da take ciki hari a kan hanyarta daga Keffi zuwa Lafia.
Rahotanni sun ce Habiba tana komawa Lafia ne bayan halartar bikin kammala karatun wata kawarta a Keffi, lokacin da wasu da ake zargin masu fashi da makami suka tare hanya tare da harbin motar da take ciki.
Lamarin ya yi sanadin rasuwar dalibar a wurin, abin da ya jefa iyalanta, abokan karatunta da sauran al’ummar Jihar Nasarawa cikin alhini. Habiba daliba ce a Sashen Chemistry na FULAFIA.
Bayan faruwar lamarin, an sake yin kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙoƙarin kare matafiya a hanyoyin jihar, musamman ɗalibai da sauran masu amfani da hanyoyin tsakanin Keffi da Lafia.
#Danmasaniradio #FULAFIA #HabibaUmmiLele #Nasarawa #Lafia #Keffi #Tsaro #Dalibai #NigeriaNews #HausaNews
