Babu inda na ce kar sojoji su karɓi ƙarin albashin da gwamnati ta yi musu sai bayan zaɓe - Obi
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya musanta rahotannin da ke cewa ya shawarci sojojin Najeriya da su ƙi karɓar ƙarin albashi da gwamnatin Najeriya ta yi musu har sai zuwa bayan zaɓen 2027.
A saƙon da ya wallafa a shafin sa na Facebook Obi ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya maras tushe, inda ya buƙaci ƴan Nijeriya da su yi watsi da shi.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce abin da ya nuna damuwa a kai shi ne yadda wasu sojoji suka rasa rayukansu sakamakon jinkirin kai musu ɗaukin gaggawa yayin da suke fuskantar hare-haren ’yan ta’adda.
Ya ce har yanzu yana mutunta jami’an tsaron Najeriya, musamman sojojin ƙasa, bisa la’akari da irin ƙalubalen da suke fuskanta wajen kare ƙasar.
Obi ya ƙara da cewa ya kasance yana kira ga gwamnati da ta samar wa jami’an tsaro da isassun kayan aiki, kulawa da kariyar da suke buƙata domin gudanar da ayyukansu.
Ya ce idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa, jin daɗin jami’an tsaro, samar musu da kayan aiki da kuma kare rayukansu za su kasance cikin abubuwan da gwamnatinsa za ta bai wa muhimmanci.
Obi ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da rahoton da ya ce an yaɗa shi ta hanyar da ba ta dace ba, tare da jaddada cewa manufarsa ita ce samar da ingantaccen tsaro da kuma kyautata rayuwar ’yan Najeriya.
