DSS ta saki kafintan da aka kama bisa zargin hannu a sace daliban Oyo sanan ta bashi diyyar Naira miliyan 3

 Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (DSS) ta saki wani kafinta mai suna Mustapha Marwana, bayan bincike ya tabbatar da cewa ba shi da hannu a satar ɗalibai da malamai da aka yi a jihar Oyo.



Marwana, wanda aka haifa a Katsina, an kama shi ne bisa zargin yana da alaƙa da harin da ’yan ta’addan Ansaru suka kai wasu makarantu a Oriire, inda aka sace ɗalibai 39 da malamai bakwai.


Bayan gudanar da cikakken bincike, wani kwamiti na DSS ya gano cewa babu wata hujja da ke nuna Marwana ɗan ƙungiyar Ansaru ne ko kuma yana da hannu wajen tallafa mata ko gudanar da ayyukanta.


Saboda haka, Darakta-Janar na DSS, Tosin Ajayi, ya bayar da umarnin a sake shi tare da ba shi Naira miliyan 3 a matsayin tallafin diyya domin taimaka masa wajen komawa rayuwarsa da sana’arsa.


An saki Marwana ga lauyansa, Oghene Forgive, wanda ya yaba da matakin DSS na tabbatar da rashin laifin wanda yake karewa.


Harin na Oriire ya faru ne a ranar 15 ga Mayu, inda aka sace mutane 46, sannan aka kashe biyu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su kafin a kuɓutar da sauran a ranar 10 ga Yuli ta hanyar wani samame na sojoji.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org