Wata ƙungiya ta karrama Kwankwaso akan kishin ƙasa da ingantaccen jagoranci a dimokuraɗiyya

 An karrama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da lambar yabo ta Patriotism and Democratic Leadership Award saboda gudunmawar da ya bayar wajen inganta dimokuraɗiyya, shugabanci nagari da hidimar jama'a a Najeriya.


An ba Kwankwaso lambar yabon ne a ranar 28 ga Yuli, 2026, ta hannun The Patriots Forum (PF) tare da haɗin gwiwar hukumar wayar da kai ta ƙasa wato National Orientation Agency (NOA).

Babban hadimin Kwankwaso a fannin yaɗa labarai, Saifullahi Hassan ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.


@Daily Nigerian Hausa 

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org