DSS ta kama babban na hannun daman Shekau - Rahoto
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama Khalid Albarnawi, wani babban jagoran ƙungiyar Ansaru da ake zargin ta sake haɗewa da Boko Haram.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa wani ɗan jarida mai bibiyar harkokin Boko Haram, Ahmad Salkida, ya ce an kama Albarnawi ne a Lokoja, jihar Kogi, kafin daga bisani a tura shi zuwa wani wuri a ranar Juma'a.
Rahoton ya ce Albarnawi na daga cikin fitattun shugabannin ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a Najeriya, kuma masana yaki da ta'addanci na kallonsa a matsayin mutum mai muhimmanci kamar tsohon shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau.
An kuma ce yana da alaƙa da wasu ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a Arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya, tare da zargin cewa ya sasanta da shugabannin ISWAP.
Salkida ya bayyana kamen a shafinsa na X (tsohon Twitter) a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin da hukumomin tsaron Najeriya suka samu a yaƙi da ta'addanci.
Sai dai ƙoƙarin samun tabbaci daga DSS da gwamnatin tarayya bai yi nasara ba, domin jami'an da aka tuntuɓa sun ƙi yin tsokaci kan rahoton.
