Zargin takardar bogi: Kotu ta bada belin tsohon minista Uche Nnaji beli kan Naira miliyan 20

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada belin tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, kan Naira miliyan 20 bayan ya musanta tuhume-tuhume shida da hukumar ICPC ta shigar a kansa kan zargin amfani da takardar shaidar karatu ta bogi da kuma almundahanar kuɗi.


Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta umarci Nnaji ya gabatar da mai tsaya masa guda ɗaya, ma'aikacin gwamnatin tarayya mai matsayi daga  mataki na 15 zuwa sama, tare da wasu sharuɗɗan kotu.


An ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar 21 ga Satumba, 2026, domin fara cikakkiyar shari'a.


ICPC ta ce an kama Nnaji ne bayan ya ƙi amsa gayyatar hukumar, yayin da ake zarginsa da gabatar da takardun shaidar karatu na bogi lokacin da aka tantance shi domin nada shi minista.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org