An kashe fitaccen shugaban ’yan bindiga Sani Yellow a Zamfara

 Rahotanni sun bayyana cewa dakarun tsaro na haɗaka da ke taimakawa jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma sun kashe wani fitaccen shugaban ’yan bindiga da aka fi sani da Kachalla Sani Yellow a Jihar Zamfara.



Majiyoyin tsaro sun shaida cewa an kashe Sani Yellow ne bayan wani shiri na musamman da aka gudanar bisa bayanan sirri da aka samu daga mazauna yankin, inda aka yi masa kwanton ɓauna yayin da ake zargin ya je wata kasuwa domin karɓar kuɗaɗen shanun da aka sace da kuma kuɗin fansa daga wasu da aka yi garkuwa da su.


Rahotannin sun ce bayan kashe shi, wasu daga cikin dakarun haɗakar sun ja gawarsa a kan babur yayin da suke gudanar da abin da suka kira murnar nasarar da suka samu kan ɗaya daga cikin shugabannin ’yan bindigar da suka fi addabar yankin.


Majiyoyi sun bayyana cewa rundunar haɗakar ta ƙunshi masu sa-kai daga al’umma da kuma wasu tsofaffin mayaƙan Boko Haram da suka tuba, waɗanda ke aiki tare da jami’an tsaro a wasu yankunan domin tattara bayanan sirri da kuma kai farmaki kan ƙungiyoyin ’yan bindiga.


An bayyana Sani Yellow a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin ’yan bindiga da ke gudanar da hare-hare a dazukan ƙananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Maru da wasu sassan Jihar Zamfara.


Ana zarginsa da jagorantar hare-haren da suka yi sanadin rasa rayuka, sace mutane domin neman kuɗin fansa, satar dabbobi da kuma tilasta dubban mazauna karkara barin muhallansu.


Wasu majiyoyin al’umma sun kuma yi zargin cewa ƙungiyar tasa na cin zarafin waɗanda aka sace, ciki har da mata, musamman idan iyalansu sun kasa biyan kuɗin fansa.


Sani Yellow na da alaƙa da marigayi Kachalla Yellow Danbokolo, wani shahararren shugaban ’yan bindiga da aka ruwaito an kashe a shekarar 2025 tare da sama da mayaƙa 170 a wani samame da dakarun sa-kai na Yankin Shinkafi suka kai.


Jami’an tsaro sun ƙara tsaurara matakan sa ido a yankunan da lamarin ya shafa domin dakile duk wata yiwuwar harin ramuwar gayya daga sauran ’yan ƙungiyar. An kuma ƙara tura jami’an tsaro zuwa wuraren da ake ganin suna cikin haɗari domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Daga Taskar Labari 

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org