Zanga-zanga Ta Barke a Legas Kan Tsaro da Tsadar Rayuwa a Ranar Dimokuraɗiyya.

 An gudanar da zanga-zanga a wasu sassan birnin Legas a yau Juma’a, yayin da Nijeriya ke bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga Yuni, inda masu zanga-zangar suka nuna damuwa kan matsalar tsaro da kuma tsadar rayuwa da ke addabar al’ummar ƙasar.



Masu zanga-zangar, waɗanda suka haɗa da mambobin ƙungiyoyin fararen hula, matasa da ƙungiyoyin al’umma, sun fito kan tituna ɗauke da kwalaye masu ɗauke da saƙonni daban-daban, suna kira ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta ɗauki matakan gaggawa domin inganta tsaro da rage matsin tattalin arziki da ke fuskantar ‘yan ƙasa.


Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ce hauhawar farashin kayayyaki, tsadar sufuri da kuma rashin tsaro sun ƙara tsananta wahalhalun rayuwa ga miliyoyin ‘yan Najeriya, lamarin da ke sa jama’a cikin ƙunci.


Masu shirya zanga-zangar sun bayyana cewa sun zaɓi gudanar da ita ne a ranar Dimokuraɗiyya domin tunatar da gwamnati muhimmancin tabbatar da jin daɗin jama’a da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, waɗanda kundin tsarin mulkin ƙasar ya ɗora wa gwamnati nauyin samarwa.


Rahotanni sun bayyana cewar an ga jami’an tsaro sun bazama a wuraren da aka gudanar da zanga-zangar domin tabbatar da zaman lafiya da hana aukuwar wata matsala.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org