Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙara Inganta Rayuwar Yan Fansho Tare da Basu Kulawar Lafiya Kyauta
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa cikin watanni uku masu zuwa za ta ƙaddamar da sabbin tsare-tsare da za su inganta rayuwar masu fansho, ciki har da tabbatar da mafi ƙarancin kuɗin fansho da kuma samar da kulawar lafiya kyauta ga masu ritaya marasa ƙarfi.
Darakta Janar ta Hukumar Kula da Fansho ta Ƙasa (PenCom), Misis Omolola Oloworaran, ce ta bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ta ce shirin Minimum Pension Guarantee zai tabbatar da cewa babu mai fansho da zai riƙa karɓar kuɗin da bai kai matakin da gwamnati ta tanada ba.
Hakazalika, ta ce za a ƙaddamar da shirin PenCare, wanda zai bai wa tsofaffin masu ritaya marasa ƙarfi damar samun kulawar lafiya kyauta domin rage musu wahalhalun da suke fuskanta bayan ritaya.
Omolola ta ce gwamnati ta kuma sauƙaƙa tsarin gudanar da harkokin fansho ta hanyar amfani da fasahar zamani, inda yanzu ake amincewa da biyan haƙƙin masu ritaya cikin sa'o'i 48 bayan sun cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata.
Ta ce PenCom ta kuma ƙara tsaurara matakan tabbatar da cewa dukkan kamfanoni da hukumomi suna tura gudummawar fanshon ma'aikatansu yadda doka ta tanada.
A cewarta, cikin shekaru biyu da suka gabata an samu nasarar kwato sama da Naira biliyan 36 na gudummawar fansho da wasu ma'aikata ba su tura ba, adadin da ya zarce abin da aka kwato a duk shekarun baya.
Daraktar Janar ɗin ta ƙara da cewa gwamnati na ƙoƙarin faɗaɗa tsarin fansho domin ya haɗa da masu sana'o'in hannu, 'yan kasuwa, direbobi, manoma da sauran ma'aikatan da ke aiki a ɓangaren da ba na gwamnati ba ta hanyar shirin Personal Pension Plan.
Ta bayyana cewa za a kuma samar da Accredited Pension Agents a faɗin Najeriya domin kai ayyukan fansho zuwa matakin al'umma tare da samar da sabbin guraben ayyukan yi ga matasa.
Omolola ta ce PenCom na kuma nazarin hanyoyin da za a yi amfani da wani ɓangare na kuɗaɗen fansho wajen zuba jari a manyan ayyukan raya ƙasa kamar hanyoyi, wutar lantarki, noma, ilimi da lafiya, tare da tabbatar da cikakken kariya ga kuɗaɗen masu fansho.
Ta ce waɗannan matakai suna daga cikin manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da cewa duk wani ɗan Najeriya da ya yi aiki na tsawon shekaru ya samu rayuwar ritaya cikin mutunci, walwala da kariya.
Daga Aliyu Samba
