An gano gawar manomin da ake nema ruwa a jallo a jihar Kwara kuma iyalin sa sun bukaci a bi musu haƙƙin sa

 Iyalan wani manomi da ya ɓace, Abdulazeez Abiodun, wanda aka fi sani da Kebe, sun roƙi hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan yadda aka kashe shi bayan an gano gawarsa a jeji a ƙaramar hukumar Isin ta jihar Kwara.



Da ta ke zantawa da PUNCH Online a ranar Talata, ƴar sa ta biyu, Rofia Abdulazeezt , ta buƙaci hukumomin tsaro, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, kafafen yaɗa labarai da sauran 'yan Najeriya masu kishin ƙasa su tabbatar an gano waɗanda suka kashe mahaifinta tare da gurfanar da su a gaban shari'a.


Rofiat ta bayyana cewa mahaifinta ya bar gidansa da ke Isalu da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar Asabar, 11 ga watan Yulin 2026, domin zuwa gonarsa ta koko da ke Owa-Onire, inda ya fita neman abin dogaro ga iyalansa. Sai dai bai dawo gida ba a wannan rana, lamarin da ya jefa iyalansa cikin damuwa.


Ta ce bayan sun yi ta ƙoƙarin kiran wayarsa ba tare da samun nasara ba, sai suka sanar da mafarauta da mutanen gari, waɗanda suka fara neman sa.


A cewarta, lokacin da mafarautan suka isa gonar, sun tarar da babur ɗinsa kawai a wurin, amma babu shi.


Ta ƙara da cewa bayan sun ci gaba da bincike cikin dajin da ke kewaye da gonar, daga baya suka gano gawarsa.


Rofiat ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da raɗaɗi, tana mai cewa mahaifinta mutum ne mai ƙaunar iyalansa kuma manomi mai ƙwazo wanda ya fita ne domin neman abin da zai ciyar da iyalinsa.


Ta buƙaci rundunar 'yan sanda ta gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan laifi tare da gurfanar da su a kotu.


Har zuwa lokacin da aka wallafa rahoton, Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kwara ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org