Gobara ta ƙone kasuwar kayayyakin kawata gida da ofis a jihar Kano

 


Wata gobara da ta tashi a kasuwar kayayyakin amfanin gida da ofis akan titin Murtala Mohammed a jihar Kano ta ƙone ɗaukacin kasuwar ƙurmus.


Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 10 na daren jiya Alhamis, inda har lokacin haɗa wannan rahoto wutar ba ta mutu ba.


Wani mai sana’a a kasuwar ya shaida mana cewa wutar ta kone kasuwar kurkusa, inda aka yi asararkaya na miliyoyin Naira.


A cewar sa, har yanzu ba su tantance sanadin wutar ba, inda ya kara da cewa suna dai tsaye suna jimami yayin da jami’an hukumar kashe gobara ke kokarin shawo kan lamarin.


Ya kara da cewa wutar ta haura zuwa ginin kamfanin aika sako na DHL da ke makwabtaka da kasuwar inda ta kama rufin Saman ginin shi ma ta kone shi.


 Kasuwar, wacce ta ke tsakanin ginin DHL da bankin FCMB a titin Murtala Muhammad, guri ne da ake sayar da kayan amfani da kawata gida da su ka.hada da harshe, kujeru, kafet, AC, katifu, firinji, talabijin da kuma kayan kawata ofis.


Kasuwar ta dade a wannan waje sama da shekaru talatin.

@Daily Nigerian Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org