Ƴansanda sun gurfanar da masu ababen hawa 123 a Kano kan amfani da motocin da ba su da lamba

 Rundunar  ƴansandan Jihar Kano ta ce ta gurfanar da direbobi 123 a gaban kotu bayan kama su da laifin amfani da motocin da ba su da lambar rajista, ko kuma masu lambar da aka rufe  a karkashin aikin "Operation Clean Plates."



Kwamishinan 'yansandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar ranar Litinin a hedikwatar rundunar da ke Bompai.


Ya ce tun bayan kaddamar da aikin a ranar 6 ga Yuli, jami'an rundunar sun kama motoci 123 da su ka karya doka a kananan hukumomi 44 na jihar, inda aka gurfanar da dukkan direbobinsu domin fuskantar hukunci bisa tanadin doka.


Bakori ya bayyana cewa manufar aikin ita ce dakile amfani da motocin da ba su da cikakkiyar shaidar rajista, yana mai cewa masu aikata laifuka na amfani da irin wadannan motoci wajen boye asalinsu da kauce wa kama su.


A wani babban ci gaba da rundunar ta samu, Kwamishinan 'yansandan ya ce jami'an ofishin 'yansanda na Panshekara sun kama wani mutum mai suna Mahi Ibrahim, mai shekaru 51 daga unguwar Rijiyar Zaki, bayan ya ki tsayawa yayin da ake binciken wata mota da ba ta da lamba  a ranar 9 ga Yuli.


Ya ce bayan binciken motar, jami'an sun kwato bindigar Beretta guda daya, busassun ganyen da ake zargin tabar wiwi ne, wuka, wayoyin lantarki, batir na lithium guda 120 da kuma wata mota da ake zargin ta sata ce ko kuma an kwato ta daga hannun barayi.


A cewarsa, an mika wanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka (CID) domin ci gaba da bincike, yayin da ake kokarin gano asalin bindigar da sauran kayayyakin domin bankado duk wata kungiyar masu aikata laifuka da ke da alaka da lamarin.


Bakori ya ce wannan kamen ya tabbatar da dalilin da ya sa rundunar ta kaddamar da Operation Clean Plates, yana mai cewa masu aikata laifuka na amfani da motocin da ba su da sahihin lamba wajen safarar makamai, miyagun kwayoyi da sauran haramtattun kayayyaki.


Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da fadada aikin a fadin kananan hukumomi 44 na jihar, tare da kira ga masu ababen hawa su tabbatar da cewa motocinsu suna da ingantacciyar rajista da kuma lambobin mota da ake iya gani a fili.


Haka kuma, ya bukaci al'ummar jihar su ci gaba da bai wa jami'an tsaro hadin kai tare da bayar da sahihan bayanan sirri, yana mai gargadin cewa duk wani jami'in da ya aikata rashin da'a za a iya kai karar sa ta lambobin Sashen Karbar Korafe-korafe na rundunar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org