Shekara Ɗaya Bayan Rasuwarsa, Tinubu Ya Ce Har Yanzu Rayuwar Buhari Na Ci Gaba Da Zaburar Da 'Yan Najeriya
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa duk da cikar shekara guda da rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, rayuwarsa da kyawawan halayensa na ci gaba da zaburar da 'yan Najeriya.
Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilta a taron tunawa da Buhari da aka gudanar a Abuja, ya bayyana marigayin a matsayin gwarzon ƙasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bautawa Najeriya cikin gaskiya, riƙon amana da kishin ƙasa.
Ya ce gudummawar da Buhari ya bayar wajen gina ƙasa ba za ta taɓa mantuwa ba, yana mai jaddada cewa dabi'unsa na gaskiya, ladabi, jajircewa da kishin ƙasa za su ci gaba da zama abin koyi ga al'ummomi masu zuwa.
Shugaban ya yi kira ga 'yan Najeriya da su rungumi kyawawan ɗabi'u irin na Buhari, musamman gaskiya, sadaukarwa da kishin ƙasa, domin ci gaban Najeriya.
Taron tunawa da marigayi Buhari ya samu halartar manyan jami'an gwamnati, tsofaffin shugabanni, 'yan siyasa, iyalansa da sauran manyan baƙi, inda aka yi masa addu'o'in Allah Ya jikansa da rahama, Ya kuma ba shi Aljannatul Firdausi.
ATP Hausa
