NSA Ribadu Ya Karɓi Babbar Tawagar Amurka, Ya Jaddada Ƙarfafa Haɗin Gwiwar Tsaro
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa Najeriya na ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwarta da Amurka, yayin da ya karɓi wata babbar tawaga daga ƙasar ƙarƙashin jagorancin sabon Mataimakin Sakataren Harkokin Afirka na Amurka, Frank Garcia.
A cewar Ribadu, wannan ita ce ziyarar farko da Frank Garcia ya kai Najeriya a hukumance tun bayan da ya hau muƙaminsa.
Ya ce ganawar ta mayar da hankali kan ƙara ƙarfafa dangantakar da ta daɗe tsakanin Najeriya da Amurka, tare da yin nazari kan irin ci gaban da Kwamitin Haɗin Gwiwa (Joint Working Group) ya samu.
Ribadu ya ƙara da cewa bangarorin biyu sun sake jaddada aniyarsu ta ci gaba da zurfafa tattaunawa, faɗaɗa haɗin gwiwa, da kuma ƙarfafa haɗin kai wajen magance matsalolin tsaro da sauran batutuwan da suka shafi muradun ƙasashen biyu.

