CDP #HANNU_DA_HANNU: Kwalliya Tana Biyan Kuɗin Sabulu
Kwana biyu bamu taɓo zancen CDP ba, ba kuma don babu abin cewar ba, a'a, Gwamnan jihar Katsina State Government, Dr. Dikko Umaru Radda ne da kan shi, ya kafa kwamitoci guda ukku tare da umurtar su da su zagaya ƙananan hukumomin dake jihar nan, domin su gana da al'umma, musamman wakilan al'umma dake cikin kwamitocin gundumomi (CLC), waɗanda gudanarwa da nasarar shirin CDP ta ta'allaƙa a kan su, tare kuma da kishi da jajircewa da suke sanyawa a cikin aikin.
Kwamiti na farko wanda aka ɗora ma alhakin ganawa da al'ummar shiyyar Daura, yana ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma'aikata na Fadar Gwamnatin jiha, Honorabul Abdulkadir M Nasir.
Sai kwamiti na biyu wanda ya zagaya shiyyar Katsina, shi kuma Sakataren Gwamnatin jiha Maigirma Barista Abdullahi Garba Faskari ya jagorance shi.
Kwamiti na ukku kuwa, wanda ke ƙarƙashin Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin jiha Alhaji Falalu Bawale, shi ya karaɗe yankin Karaɗuwa, shiyyar Funtua ke nan.
Waɗannan kwamitoci sun zagaya kuma sun ji ta bakin al'umma, irin rawar da wannan shiri na CDP #hannu_da_hannu yake takawa da kuma yadda yake taɓawa tare da inganta rayuwar al'umma a yankin gundumomin dake jihar nan.
A wannan rubutu, babu buƙatar bayanin yadda wannan shiri yake tafiya da kuma yadda jagoran shirin Assoc Prof Kamaluddeen Kabir Katsina da Muƙarraban shi, suke tsaye wajen ganin sun sauke nauyin da ya rataya a kan su.
Wannan rubutu na yau, manufar shi ita ce Maikaratu ya fahimci yadda CDP ta sami karɓuwa ta kuma shiga zukatan al'ummar wannan jiha, wanda hakan ya samu ne ta yadda aka shigo da al'umma, kai tsaye, cikin hidimar ingantawa da kyautata rayuwar su. Ta yadda su ke faɗin buƙatun su, kuma su ake ba dama su biya ma kan su buƙatun. Iyaka gwamnati ta bada kuɗi kuma tasa ido tare da tabbatar da kwalliya na biyan kuɗin sabulu.
Ba zan ja Maikaratu da rattabo jawaban da sukai ta gudana wajen waɗancan tarukan da akayi yayin wancan rangadi ba, amma zan shaida maka cewa, tun zamanin tsohon shugaba Janar Ibrahim Babangida, da ya ƙirƙiri wata hukuma a lokacin shi, wadda aka fi sani da Difiri (DFRRI, Directorate of Foods, Roads and Rural Infrastructure), wadda ta riƙa shiga lungu da saƙon wannan ƙasa domin samar da abubuwan more rayuwa ga al'umma, ba a ƙara samun wata da ta kai ga al'umma ba kai tsaye, sai CDP #Hannu_Da_Hannu.
Duk da tasirin da waccan hukumar tayi, bai kai irin na CDPn mu ba, domin ita Difiri ayyuka ta riƙa yi ma al'umma daidai yadda ta ga ya dace, ita kuwa CDP, al'umma ne da kan su suke faɗin buƙatun su kuma a basu dama su share ma kansu hawaye.
Kamar yadda muke ta bayani, al'umma baki ɗaya su ke gaban CDP ba 'yan jam'iyyar APC ba kaɗai. Shi yasa har akai tarukan nan aka gama, maganar al'umma ake, ba siyasa ba. Wannnan kuma ya sanya, a hukumance, babu wakilcin jam'iyya mai mulki, sai dai iyayen ƙasa da shuwagabannin al'umma, wanda suka haɗa da Hakimmai da Magaddai, Limamai, Dattawa har ma da 'yan kasuwar mu.
Ga wanda Allah Ya ba iko, sai ya bibiyi shafin mu domin samun jawabai kan CDP daga bakunan al'ummar mu da suka rungumi wannan shiri kuma suka ga amfanu da ingancin shi.
CDPn nan dai ta tabbata ta kowan ce, kamar yadda mukai ta faɗi. An yi ta ne don Al'umma su zamo suna da ruwa da tsaki na gaske, kuma a aikace, cikin hidimar tafiyar da gwamnati, musamman abinda ya shafi jin daɗi da walwalar su.
Ya Allah muna roƙon Ka inganta wannan shiri, sakamakon nasarar shi ta zarce tunanin duk mai hasashe, hatta waɗanda suka kawo shi da masu tafiyar dashi.
Ya Allah Kai mana maganin abinda ya ishe mu.
Ga mai son ji da ganin yadda wannan rangadi ya kasance, sai a latsa; Katsina State Community Development Programme
Daga Abdulhadi Ahmad Bawa

