Mutum ɗaya ya mutu yayin da bakwai su ka jikkata bayan wani sashi na ginin majalisar dokoki ta Gombe ya rufta

 Mutum ɗaya ya rasu yayin da wasu ma'aikata bakwai suka jikkata sakamakon ruftawar wani sashe na sabon ginin majalisar dokokin Jihar Gombe da ake ginawa.



Gwamnatin Jihar Gombe ta ce lamarin ya faru ne ranar Juma'a bayan wani ɓangare na ƙofar shiga  ya rufta a wurin aikin, inda lamarin ya rutsa da ma'aikata takwas.

Sanarwar da babban sakataren ma'aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri, Danladi Adamu, ya sanya wa hannu ta ce an garzaya da waɗanda suka jikkata asibiti, inda biyar ke karɓar magani a Asibitin Kwararru na Gombe, yayin da biyu ke Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) da ke Gombe.


Gwamna Inuwa Yahaya ya jajanta wa iyalan mamacin, tare da umartar gwamnati ta ɗauki nauyin kula da lafiyar dukkan waɗanda suka jikkata.


Haka kuma ya ba da umarnin a gudanar da bincike cikin gaggawa domin gano musabbabin hatsarin, tare da umartar kamfanin da ke aikin da masu ba da shawara kan aikin su gabatar da rahoton abin da ya faru cikin sa'o'i 24.


Gwamnatin jihar ta ce matakan da za ta ɗauka za su dogara ne da sakamakon binciken, tare da jaddada aniyarta na tabbatar da bin ƙa'idojin tsaro da inganci wajen aiwatar da ayyukan gine-ginen gwamnati.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org