Ɗan wasan ƙasar Afirka ta Kudu Jayden Adams ya rasu kwanaki bayan buga gasar kofin duniya
Ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar Mamelodi Sundowns da tawagar ƙasar Afirka ta Kudu, Jayden Adams, ya rasu yana da shekaru 25.
An gano gawarsa a safiyar Asabar a wani gini da ke Schotschekloof a birnin Cape Town, yayin da har yanzu ba a bayyana musabbabin rasuwarsa ba.
Rasuwar Adams ta zo ne kwanaki kaɗan bayan mutuwar kakarsa mai shekaru 72, Marianna Adams, wadda ta rasu kafin wasan rukuni na Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Czech a gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2026. Duk da alhinin da yake ciki, Adams ya ci gaba da buga wa ƙasarsa wasa a gasar.
Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF), Ministan Wasanni na Afirka ta Kudu da Ƙungiyar 'Yan Wasan Kwallon Kafar ƙasar sun bayyana alhininsu kan rasuwar, suna mai cewa ƙasar ta yi babban rashi.
Adams ya taka rawa wajen taimaka wa Afirka ta Kudu tsallake matakin rukuni na gasar cin kofin duniya a karon farko, sannan ya taimaka wa Mamelodi Sundowns lashe kofin Zakarun Nahiyar Afirka a kakar 2025/26.
