Yan Bindiga Sun Sace Dalibai 7 A Zamfara.
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da dalibai shida na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic) da ke Kaura Namoda a Jihar Zamfara, bayan sun kai hari gidan da daliban ke zaune a wajen harabar makarantar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a wani gida da ke gefen unguwar Low-Cost a garin Kaura Namoda, inda maharan suka kutsa cikin gidan tare da yin awon gaba da daliban.
Shugaban Karamar Hukumar Kaura Namoda, Alhaji Mannir Haidara Kaura, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da ayyukan ceto domin tabbatar da kubutar da daliban cikin koshin lafiya.
“Lamarin ya faru, kuma jami’an tsaro suna ci gaba da gudanar da aiki domin ceto daliban da aka sace tare da mayar da su ga iyalansu lafiya,” in ji shi.
Wani dalibi a makarantar, Ibrahim Ahmad, ya bayyana cewa daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ya samu damar kubuta daga hannun maharan, lamarin da ya rage adadin wadanda ke tsare zuwa shida, wadanda suka hada da maza uku da mata uku.
Ita ma Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin. Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce jami’an rundunar tare da dakarun Operation Fansan Yamma sun fara wani samame na musamman domin ceto daliban.
