Ƙungiyar lauyoyi ta yi suka kan tsauraran sharuɗɗan beli da alkalai ke gindayawa

 Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta nuna damuwa kan yadda kotuna da jami’an tsaro ke sanya tsauraran sharuɗɗan beli da ke hana mutane da dama samun ‘yancinsu duk da an amince musu da beli.


Shugaban NBA, Afam Osigwe, ya bayyana cewa yawan buƙatar masu tsaya wa wanda ake tuhuma su kasance manyan ma’aikatan gwamnati ko kuma mallakar kadarori masu tsada ya mayar da beli tamkar wata hanyar tsare mutum kafin a yanke masa hukunci.


Ya ce hakan na tauye haƙƙin ‘yanci da kundin tsarin mulki ya tanada tare da karya ka’idar cewa wanda ake tuhuma ba shi da laifi har sai an same shi da laifi a kotu.


Osigwe ya jaddada cewa manufar beli ita ce tabbatar da halartar wanda ake tuhuma a kotu, ba hukunta shi kafin a same shi da laifi ba. Ya kuma buƙaci kotuna da su tabbatar da cewa sharuɗɗan beli sun kasance masu sauƙi, adalci kuma masu yiwuwa a cika su ga wanda ake tuhuma.


Daily Nigerian

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org