KASSAROTA Ta Sanya Sabbin Dokoki Ga Manyan Motocin Daukar Kaya a Katsina
Hukumar Kula da Tsaro da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Katsina (KASSAROTA) ta fitar da sabbin dokoki da ka’idoji ga masu manyan motocin daukar kaya, tireloli da wuraren sauke kaya a fadin jihar, a wani yunkuri na rage cunkoso, inganta tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma
A cikin wata sanarwa da Sakataren Hukumar, Al-Amin Batsari, ya fitar ranar Alhamis, hukumar ta ce ta lura da karuwar yawan manyan motocin da ke shiga birnin Katsina da sauran manyan garuruwan jihar. Ta bayyana cewa duk da irin gudummawar da hakan ke bayarwa wajen bunkasa tattalin arziki, amma akwai bukatar samar da tsari da dokoki domin kauce wa matsalolin zirga-zirga da kiyaye hadurra.
A cewar Batsari, Sabbin dokokin sun tanadi cewa duk wata babbar mota da za ta shiga gari domin sauke kaya ko daukar kaya dole ne ta yi hakan tsakanin karfe 9:00 na dare zuwa karfe 9:00 na safe, lokacin da zirga-zirga ba ta da yawa. Hukumar ta kuma umurci direbobi da masu motocin da su tabbatar da cewa sun ajiye motocinsu a wuraren da ba za su hana zirga-zirga ko mamaye hanyoyin jama’a ba.
Dangane da motocin da suka lalace a kan hanya kuwa, KASSAROTA ta ce wajibi ne mai mota ko wakilinsa ya sanar da hukumar cikin gaggawa domin daukar matakan da suka dace na kawar da cikas da kare masu amfani da hanya. Haka kuma, duk wani aikin sauke kaya ko daukar kaya da zai shafi zirga-zirgar jama’a ko amfani da wani bangare na hanya dole ne a fara neman amincewar hukumar kafin a gudanar da shi.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa duk manyan motocin da ke shiga jihar domin wucewa zuwa wasu garuruwa ko jihohi ba tare da wata bukata a cikin birnin Katsina ba, wajibi ne su rika amfani da hanyoyin ratse (Ring Road) da gwamnatin jihar ta samar, maimakon shiga cikin gari kaitsaye.
KASSAROTA ta nuna damuwa kan yadda wasu manyan motocin ke tafiya da gudun da ya wuce ka’ida musamman a titin Kwado da Ring Road, tana mai gargadin cewa irin wannan hali na jefa rayukan jama’a cikin hadari.
Hukumar ta ce dukkan manyan motocin da ke gudanar da harkokin daukar kaya za su ci gaba da biyan kudin Waybill da sauran kudaden da doka ta tanada.
A cewar hukumar, duk wanda ya karya daya daga cikin wadannan dokoki zai fuskanci tarar naira 50,000 tare da sauran matakan hukunci da suka hada da kama abin hawa, dakatar da ayyukan motar ko duk wani hukunci da dokokin jihar suka tanada.
Hukumar ta bayyana cewa matakin na daga cikin kokarin gwamnati na tabbatar da ingantacciyar zirga-zirga, rage hadurran hanyoyi da kuma kiyaye lafiyar hanyoyin jihar Katsina
