Tambayoyin Da Har Yanzu Peter Obi Bai Bawa Yan Najeriya Amsarsu Ba
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya shafe shekaru yana gina sunansa a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu sukar yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati a Najeriya. Amma yayin da yake neman amincewar ‘yan ƙasa a matsayin madadin shugabanci, wasu kalamansa da matsayinsa kan batutuwan tsaro na ci gaba da tayar da tambayoyi.
Ɗaya daga cikin batutuwan da suka fi janyo ce-ce-ku-ce shi ne matsayinsa kan ƙungiyar IPOB (Indigenous People of Biafra). A wata hira da ya yi a shekarar 2022, Obi ya bayyana cewa bai yarda da ayyana IPOB a matsayin ƙungiyar ta’addanci ba.
Ya ce:”Abin da kawai ban yarda da shi ba shi ne kiran IPOB ƙungiyar ta’addanci; su ba ‘yan ta’adda ba ne. Ina zaune a Onitsha kuma kullum ina haduwa da su
Wannan furuci ya sake komawa kan gaba a tattaunawar siyasa yayin da Najeriya ke ci gaba da fama da matsalolin rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.
