An Gudanar da Taron Masu mukamai da Sarautun Gargajiya Na Gundumar jibia da Daddara
Taron Wanda Sabon Galadiman Jibia Alhaji Saminu Salu jibia ya Assasa ya gudana a Dakin Taro Na karamar hukumar jibia ya Samu halartar Hakimin jibia Alhaji Rabe Rabi'u jibia da Takwaransa Na Daddara Alhaji Usman Usman Na Goggo da wakilin kwamishinan kananan hukumomin jahar katsina da wasu daga cikin magaddan Gundumar Daddara da jibia da Masu mukaman Sarautun Gargajiya Na Gundumomin.
Daga cikin Masu Mukamai da suka halarci Taron akwai; Sarkin Malaman jibia Alhaji Ibrahim Sabi'u da wazirin jibia Alhaji Hamza Sale Marini Jibia da Matawallen Daddara Alhaji Kabir Salisu Dan Hizba da Sarkin Noman Jibia Alhaji Ibrahim Lawal sefa da Sarkin Tsabtar Jibia da Sarkin fadan jibia Alhaji Salisu Garba kwangee da Sarkin Hawan jibia Yusuf Mai kudi jibia da Sarkin Bakin jibia da Jagaban jibia Alhaji Sada Ahmad da Hardon fulanin daji da Shugaban kungiyar miyatti Allah da sauransu.
Maqasudin wannan taron kamar yadda Shugaban kungiyar Alh Saminu Salu Galadiman Jibia ya baiyana, Shi ne; Don a zaburar da Masu mukaman Sarautun Gargajiya Na Gundumar jibia da Daddara su kara fahimtar muhimmancinsu da amfaninsu ga rayuwar al'ummah baki Daya.
