Hukumar Tace Fina-finai ta Kano ta dakatar da Amina Uba Hassan da Rabagardama na shekara guda.
Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta dakatar da fitattun jaruman Kannywood biyu, Amina Uba Hassan da Adam Garba wanda aka fi sani da Rabagardama, daga gudanar da harkokin fim a jihar har na tsawon shekara guda.
Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne bayan bayyanar jaruman a wani bidiyo da ta bayyana a matsayin wanda ya saɓa da tarbiyya da ƙa’idojin ɗabi’a, lamarin da ya haddasa ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar jihar Kano.
A cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 16 ga Mayu, 2026, wadda Jaridar Taskar Labarai ta ci karo da ita, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya ce an fitar da sanarwar ne a madadin shugaban hukumar, Malam Abba El-Mustapha.
Sanarwar ta bayyana cewa dakatarwar na nufin an hana jaruman biyu shiga ko gudanar da duk wani aikin fim a Jihar Kano na tsawon shekara guda.
Hukumar ta ƙara da cewa dokarta ta ba ta ikon dakatar da duk wani ɗanmasana’antar Kannywood da ya karya ƙa’idojin da aka shimfiɗa, tare da gargadin cewa karya umarnin dakatarwar na iya jawo hukunci mai tsauri a ƙarƙashin doka.
A cewar hukumar, matakin na daga cikin ƙoƙarin da take yi na tabbatar da tsaftace tarbiyya da kuma kare martabar masana’antar shirya fina-finan Hausa.
Da yake jawabi kan lamarin, shugaban hukumar, Malam Abba El-Mustapha, ya yi kira ga jarumai da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood da su guji duk wani abu da ka iya zubar da mutuncin masana’antar ko rage mata kima a idon al’umma.
Ya kuma gargadi masu shirya fina-finai da daraktoci da su mutunta umarnin dakatarwar, yana mai cewa yin aiki da waɗanda aka dakatar tamkar ƙalubalantar dokar hukumar ne kai tsaye.
Rahotanni sun ce bidiyon da ya jawo ce-ce-ku-cen na da alaƙa da wani sabon shirin fim mai suna Har Abadan, wanda hukumar ta ce wasu daga cikin abubuwan da ke cikinsa sun saɓa da tarbiyyar al’ummar Kano.
Jaridar Taskar Labari

