AN YI KIRA GA GWAMNATI DA MASU HANNU DA SHUNI SU SAMAR DA MATSUGUNI NA DINDINDIN GA MAKARATAR MADRASATUL ULUL-ALBAB LITTAHAFIZIL QUR’AN WAD-DARASATUL ISLAMIYYA MAKERA, FUNTUA A JIHAR KATSINA
Shugaban makarantar Ustaz Malam Al’amin Rashid, ya yi wanna kiran a yayin bikin taya murna ga dalibai goma da suka haddace izu goma na Alkur’ani Mai Girma a Makarantar.
Ya kara da cewa, an kafa makarantar ne da taimakon Malam Yahaya Ahmad, ma’aikaci a sahen binciken kudi na jihar Katsina, Inda yake dinka wa daliban makarantar kayan makaranta, tare da biyan kudin makaranta da kuma alawus-alawus na malaman makarantar a kowane wata.
Shugaban makarantar ya ce daga lokacin da aka kafa makarantar kawo yanzu, makarantar tana da dalibai 53, azuzuwa biyar da malamai hudu.
A jawabansu daban-daban, Daraktan makarantar, Alhaji Yahaya Ahmad, da Headmaster din makarantar, Malama Aisha Haruna, sun bayyana godiyar su ga marigayi Alhaji Lawal Garba Gwandu da iyalansa, kasancewar shi ne mutum na farko da ya ba makarantar matsuguni na wucin gadi.
Alhaji Yahaya Ahmad da Malama Binta sun mika godiya ga Sadaukin Kudun Katsina, Alhaji Jamilu Haruna, bisaga gina masallci a makarantar wanda shima masallcin ana amfani daji a matsayin wurin koyar da daliban makaratar.
Alhaji Yahaya Ahmad ya yaba wa malaman makarantar bisa kokarin da suke yi wajen koyar da yara ilimi tare da tarbiyya mai kyau. Haka kuma ya gode wa makwabta da daukacin masu taimaka wa makarantar.
