KANKARA: Gwamna Radda Ya Ziyarci Hakimin Kankara, Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatinsa na Ci Gaba da Ayyukan Alheri a Jihar Katsina

A rana ta takwas na gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Dikko na 2027, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kai ziyarar girmamawa ga Sarkin Pauwan Katsina kuma Hakimin Kankara, Justice Alhaji Adamu Bello.



Ziyarar ta biyo bayan gagarumar nasarar da aka samu a Kafur, inda ta ƙara tabbatar da al’adar tawagar yaƙin neman zaɓen na kai ziyara da tattaunawa da sarakunan gargajiya da shugabannin addini a dukkan wuraren da ta ziyarta.


A yayin ziyarar, Gwamna Radda ya bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu a Kankara, waɗanda suka haɗa da gyaran Babban Asibitin Kankara, inganta cibiyoyin kiwon lafiya, gyaran makarantu, tallafin noma, shirye-shiryen bunƙasa al’umma da inganta tsaro.


Gwamnan ya kuma jaddada kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da Mataimakinsa, Malam Faruk Lawal Jobe, wanda ya fito daga Karamar Hukumar Kankara, tare da bayyana matakan da gwamnatinsa ta ɗauka na ƙarfafa hukumomin gargajiya da na addini, ciki har da amincewa da biyan alawus na wata-wata ga masu gari da limaman addini.


Ya yi kira ga al’ummar Kankara da su ci gaba da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC baya domin samun nasara a zaɓen 2027.


A nasa jawabin, Justice Alhaji Adamu Bello ya yaba wa Gwamna Radda bisa ayyukan raya ƙasa da gyare-gyare da shirye-shiryen da gwamnatinsa ta aiwatar a Kankara, musamman inganta tsaro, ilimi, kiwon lafiya, tallafin karatu da Shirin Bunƙasa Al’umma (CDP).


Ya kuma nuna godiyarsa ga Gwamnan bisa damar ci gaba da ya samar wa al’ummar Kankara.


Tawagar yakin neman zaben ta kunshi Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Jobe, Shugaban Yakin Neman Zaben, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, Shugaban Jam’iyya, Dr. Bishir Gambo Saulawa, Alh. Mustapha Inuwa, Sakataren Tawagar, Alh Abdullahi Turaji, Sanata Muntari Dandutse, Dantakarar Danmajalisar Kankara/Faskari/Sabuwa, Hon Hamza Sule Faskari da sauran yan tawaga. 


MS Ingawa

SSA, Media & Strategy

Katsina State Government 


November 4, 2026.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org