INEC: Ba mu cire sunan Atiku daga jerin ’yan takara ba

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce har yanzu ba ta samu kwafin hukuncin kotu da ya soke shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin David Mark da kuma naɗin ’yan takararta ba.


Hukumar ta bayyana cewa ba ta cire sunan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da abokin takararsa, Rotimi Amaechi, daga shafinta na intanet ba, sabanin jita-jitar da ta yaɗu a kafafen sada zumunta.


Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da Kan Masu Zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa hukumar ba ta karɓi sahihin kwafin hukuncin kotun ba, don haka ba ta tattauna matakin da za ta ɗauka ba.


Ya ce samun sahihin kwafin hukuncin kotu na iya ɗaukar kusan mako guda, don haka ba za a sa ran hukumar ta aiwatar da hukuncin da ba ta karɓa a hukumance ba.


A ranar Alhamis ne Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya soke shugabancin ADC ƙarƙashin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, tare da rusa matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da zaɓen Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027.


Kotun ta yanke hukuncin ne bisa ƙarar da tsohon Mataimakin Shugaban ADC na Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar, yana ƙalubalantar yadda aka kafa shugabancin Mark.


Sai dai ADC ta yi watsi da hukuncin, tana mai cewa ba shi da ingantaccen tushe na shari’a, tare da bayyana aniyarta ta ɗaukaka ƙara.


Shi ma Atiku ya yi watsi da hukuncin, yana mai cewa zai ɗaukaka ƙara kuma ba zai dakatar da shirye-shiryen takararsa ta 2027 ba.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org