Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da lambar da za a nemi rancen kuɗi da kayan abinci da ba amfanin gida ta wayar hannu
Gwamnatin Tarayyar ta ƙaddamar da wani sabon tsarin bada rancen kuɗi ta hanyar amfani da lambar USSD, wanda zai bai wa ƴan ƙasa damar karɓar rancen kuɗin sayen kayayyaki ta wayoyin hannu na yau da kullum ba tare da buƙatar intanet ko wayoyin zamani ba.
Hukumar Bada Lamuni ta Ƙasa (CREDICORP) ce ta ƙaddamar da sabon shirin mai suna SPARK domin faɗaɗa damar samun rance, musamman ga mutanen da ba su taɓa karɓar rance ba ko kuma ba su da tarihin karɓa da biyan bashi a hukumance.
Hukumar ta bayyana *347*333# a matsayin lambar USSD din, sai dai har yanzu ba a tabbatar da cewa tsarin ya fara aiki a faɗin ƙasar baki ɗaya ba.
CREDICORP ta ce ana sa ran tsarin zai samu karɓuwa da kuma fara aiki a wurare da dama kafin ƙarshen shekarar 2026.
Manufar shirin ita ce bai wa masu karɓar rance damar gina tarihin biyan bashi, wanda zai taimaka wajen inganta matsayinsu na samun lamuni da kuma buɗe musu ƙofofin samun wasu hidimomin kuɗi a nan gaba.
Abubuwan da ’yan Najeriya za su iya karɓar rancen na CREDICORP ɗin sun ƙunshi manyan fannoni guda biyar da aka tsara domin taimaka wa ’yan Najeriya samun muhimman kayayyaki, kayan amfanin gida da kuma kadarorin da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.
Ga fannoni biyar ɗin:
1. Sufuri: Motocin da ke amfani da iskar CNG da motocin lantarki.
2. Kayan fasahar zamani: Kwamfutocin tafi-da-gidanka, wayoyin zamani da na'urorin kwamfutar hannu (Tablets).
3. Hanyoyin samar da makamashi: Janareto da na'urorin hasken rana (Solar panels).
4. Inganta gidaje: Kayan ɗaki, na'urorin amfanin gida da kayan gini.
5. Muhimman abubuwan rayuwa: Kiwon lafiya, tufafi, abinci da abubuwan sha.
.png)