Gwamnatin Burkina Faso Ta Sake dawo da Hukuncin Kisa

 

Gwamnatin Ƙasar Burkina Faso ta sake dawo da hukuncin kisa, bayan majalisar dokokin ƙasar ta amince da matakin baki ɗaya. Kamar yadda  Ma'aikatar Shari'a ta ƙasar ta sanar a ranar Talata da ta gabata.

Sabon kundin dokokin hukunta laifuffuka ya soke matakin da aka ɗauka a shekarar 2018 na janye hukuncin kisa. Mahukuntan ƙasar sun bayyana cewa, manufar matakin ita ce ƙarfafa zaman lafiya da bin doka, kiyaye mutuncin 6ƙasa da inganta tsaro.

Ƙasar Burkina Faso, da ke Yammacin Afirka, tana ƙarƙashin mulkin soja tun bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 2022, wanda Kyaftin Ibrahim Traoré ya jagoranta. A shekarar da ta gabata ne Traoré ya bayyana shirin sake dawo da hukuncin kisa.

A cewar kamfanin dillancin labaran gwamnatin ƙasar, laifuffukan da za su iya jawo hukuncin kisa sun haɗa da ta'addanci, leƙen asiri, cin amanar ƙasa, kashe uba da gangan, da kuma shigo da kayayyakin da  wa'adin amfani da su ya kare ko waɗanda aka haramta, idan suka haddasa mutuwa.

Sai dai matakin ya jawo damuwa daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam. Ƙungiyar Amnesty International ta taɓa buƙatar gwamnatin Burkina Faso da kada ta sake dawo da hukuncin kisa.

An gudanar da hukuncin kisa na ƙarshe da aka tabbatar a Burkina Faso ne a shekarar 1988.

Sake dawo da hukuncin kisan ya nuna gagarumin sauyi a tsarin shari'ar laifuffuka na ƙasar, tare da sake buɗe muhawara kan kare haƙƙin ɗan Adam da kuma amfani da hukuncin kisa a matsayin hukuncin laifi.

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org