Gwamna Radda Ya Gabatar Da Ayyukan Raya Kasa Da Ya Gudanar A Sabuwa, Yayin Da Ziyarci Karamar Hukumar Yau Yakin Neman Zabe.
Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda ta bayyana muhimman ayyukan raya al’umma da ake aiwatarwa a Ƙaramar Hukumar Sabuwa, waɗanda suka shafi kiwon lafiya, ilimi, noma, tsaro, hanyoyi, samar da ruwa da tallafin jin ƙai.
A fannin kiwon lafiya, an yi gyare-gyare da inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, tare da gina gidajen ma’aikata, samar da hasken lantarki da kuma katanga a cibiyoyin kiwon lafiya na Sabuwa, Mebakko, Gamji, Damari, Machika da Sayau.
A bangaren ilimi, ayyukan sun haɗa da gyaran makarantu da gina sabbin azuzuwa, ciki har da gina makarantar sakandare a Damari da Labi, da kuma gyaran makarantu a Sabuwa, Mebakko, Unguwar Sani da Dugun Muazu.
Haka kuma, gwamnati ta bayyana tallafin da take bai wa manoma ta hanyar raba takin zamani sama da buhu 10,000 a duk shekara, samar da injinan ban ruwa da sauran kayan aikin noma, tare da tallafa wa noman rani.
Dangane da tsaro, an bayyana kafa da tallafa wa rundunar sa-kai ta Community Watch Corps, da samar da babura da motoci domin ƙarfafa ayyukan tsaro a yankunan al’umma.
A bangaren hanyoyi, ana gudanar da aikin gina hanyar Sabuwa zuwa Tashar Nawa mai tsawon kilomita 27.8, tare da gyaran hanyar da ta haɗa madatsar ruwa da garin Sabuwa.
Rahoton ya kuma bayyana tallafin jin ƙai ga waɗanda suka rasa matsugunansu sakamakon rikice-rikice da mutanen da aka sako bayan sace su, da kuma rabon kayan abinci ga gidaje masu ƙaramin ƙarfi da sauran masu buƙata.
Bugu da ƙari, ana tallafa wa matasa ta hanyar cibiyar koyon sana’o’i ta Katsina Youth Craft Village (KYCV), tare da shirye-shiryen Hukumar Bunƙasa Kasuwanci ta Jihar Katsina (KASEDA) domin haɓaka sana’o’i da ƙananan kasuwanci.
A fannin samar da abubuwan more rayuwa, an kuma bayyana ayyukan samar da ruwa a al’ummomi daban-daban na Sabuwa, da gyaran manyan masallatan Juma’a na ƙungiyoyin Darika da Izala da ke garin.
Wannan bayani na cikin kundin ayyukan da aka gabatar ƙarƙashin taken Radda Fact Sheet – Sabuwa LGA, a matsayin wani ɓangare na yaɗa bayanai kan ayyukan gwamnatin jihar.
.jpeg)